IQNA

Sayyid Nasrullah Ta Hanyar Kalamansa Ya Yi Nasarar Yaki A Kan Isra’ila

21:44 - April 18, 2012
Lambar Labari: 2307895
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya samu rabin nasarar yakinsa da haramtacciyar kasar Isra’la da kalamansa na hikima ta yadda baya ga karon batta da ake yi tsakanin bangarorin biyu kalamansa suna raunana sojojin yahudawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa,masani kan harkokin sisa a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran Muhammad Shadi ya bayyana cewa, jagoran kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya samu rabin nasarar yakinsa da haramtacciyar kasar Isra’la da kalamansa na hikima ta yadda baya ga karon batta da ake yi tsakanin bangarorin biyu kalamansa suna raunana sojojin yahudawa a lokacin yakin kawanaki 33 da aka yi.
A wani bayanin na daban babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, komawa kan teburin tattaunawa tsakanin bangarorin siyasa na kasar Syria shi kadai ne mafita a rikicin da kasar ke fama da shi. Sayyid Narullah ya bayyana hakan ne a wata zantawa ta musamman da ta hada shi Julian Assange mamallakin shafin yanar gizo wikileaks, inda ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah ta tuntubi bangarorin 'yan adawar kasar Syria da su amince da batun sulhu da koma ga tattaunawa domin kawo karshen rikicin kasar, amma sun bayyana rashin amincewarsu da duk wata tattaunawar zaman lafiya.
Ya ce yayin da wasu daga cikin kasashen larabawa da wasu wadanda ban a larabawa ba suke ci gaba da aikewa da makudan kudade da makamai zuwa 'yan tawaye da suke dauke da makamai a Syria, domin wargaza duk wani shiri na zaman lafiya a Syria.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya zargi wasu daga cikin kasashen larabawa da na yammacin turai hankoron ganin sun wargaza shirin Kofi Annan na samar da zaman lafiya a Syria, ta hanyar ci gaba da azuzuta wutar rikicin kasar da aikewa da makamai ga 'yan tawaye da suke kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula.
983493
captcha