Kamfanin dillancin lbaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babbar jami’ar muslunci Azhar dake birnin Alkajira na kasar Masar ta yi kakausar suka da yin Allawadai da wasu masu neman fitina tsakanin musulmi da suke cin zarafin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar ta Masar.
A bangare guda kuma a yau ne ake fara sharai'ar mutane 75 da aka kama a kasar Masar dangance da boren da aka yi a filin wasan kollon kafar garin Port Saiid a watan Feburariru.
Za a saurari shari'ar ne a kotun tafi da gidanka da ke makarantar yan sanda a waje da birnin Alkahira maimakon gudanar da ita a garin na Port Said inda rikiicn ya faru.
A wannan kara dai ana tuhumar jamian yan sanda tara da jamian kulob din al-Masri uku, da laifukan da suka hada da kisan kai da kuma sakaci dangane da tsaro, a ranar 1 ga watan Feburariru ne rikici ya barke a filin wasan kwallon kafa na garin Port Said bayan da aka kammala wasa tsakanin kulob din al-Masry na garin da kuma kulob din al-Ahali na birnin Alkahira, kuma mutane 74 suka rasa rayukansu a sakamakon rikicin.
987575