IQNA

'Yancin Al'ummar Kasar Masar Ya Tsaya Ga Yunkurin Sojojin Kasar

22:10 - April 19, 2012
Lambar Labari: 2308204
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Masar sun yi juyin juya hali amma kuma har yanzu wannan juyi bai kai ga abin da al'umma suke fata ban a kawo karshn mulkin kama karya na husni Mubarak inda ahalin yanzu majalisar sojin kasar c eke gudanr da irin wannan mulki.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, al'ummar kasar Masar sun yi juyin juya hali amma kuma har yanzu wannan juyi bai kai ga abin da al'umma suke fata ban a kawo karshn mulkin kama karya na husni Mubarak inda ahalin yanzu majalisar sojin kasar ce ke gudanr da irin wannan mulki irin na tsohon shugaban.

Dan takarar shugabancin kasa na kungiyar Ikhwanul muslimin a Masar da hukumar zabe ta yi waje da shi Kherat Shatir, ya yi dirar mikiya kan majalisar koli ta soji da ke mulki a Masar, wanda kuma da dama daga cikin masu bin diddigin lamurran kasar sun imanin cewamajalisar sojin ba a shirye take ta mika mulki ba.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi jiya a gaban manema labarai a birnin Alkahira, Kherat Shatir ya bayyana cewa majalisar sojin kasar tana ci gaba da yin mulkin kama karya irin Husni Mubarak, wanda kuma a cewarsa al'ummar kasar Masar ba za su taba amincew da haka ba.

Shatir ya ce a ranar Juma'a mai zuwa miliyoyin magoya bayan kungiyar Ikhwanul muslimin za su fito a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira, domin nuna rashin amincewa da matakan da majalisar sojin kasar na dauka da ya kira na mulkin kama karya.

987822

captcha