IQNA

Tafiyar Babban Malami Mai Bayar Da Fatawa A Masar Zuwa Qods

20:06 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309359
Bangaren kasa da kasa, babban malamin kasar Masar mai bayar da fatawa a hukumance ya yi tafiya zuwa birnin Qods bayan da ya shirya tafiyar tare da hadin baki da ma'aikatar tsaron haramtacciyar kasar ba tare da sanin sauran malamai na kasar Masar ba.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, malamin gwmnatin kasar Masar mai bayar da fatawa a hukumance ya yi tafiya zuwa birnin Qods bayan da ya shirya tafiyar tare da hadin baki da ma'aikatar tsaron haramtacciyar kasar ba tare da sanin sauran malamai na kasar Masar ba musamman babbar jami'ar muslunci ta Azhar.

Mahukuntan haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar a huklumance cewa wannan tafiya ta zo tare da hadin baki da su, kuma malamin ya ziyarci wurare na tarihi da suke yankunan da dama da suka hada da birnin Qods mai alfarma, wanda kuma yahudawan ne suka shirya masa dukaknin yanayin tafiyar tasa, wanda hakan ya jawo babban cece kuce a tasakanin al'ummomin Masar.

Babban malamin kasar Masar mai bayar da fatawa a hukumance ya yi tafiya zuwa birnin Qods bayan da ya shirya tafiyar tare da hadin baki da ma'aikatar tsaron haramtacciyar kasar ba tare da sanin sauran malamai na kasar Masar bad a suka hada babbar jami'ar Musulunci ta kasar.

989661




captcha