IQNA

Iran Na Bayar Da Gagarumar Gudunmawa Wajen Bunkasa Ayyukan Kur’ani Ahanistan

22:36 - April 22, 2012
Lambar Labari: 2310221
Bangaren kasa da kasa, jamhuriyar musulunci ta Iran tan abayar da gagarumar gudunmawa ta fuskacin bunkasa ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar Afghanistan kamar yadda take taimaka mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke gudanar da harkokinsu a kasar.
Kamfanin dillancin labarann iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin malaman addinin muslunci na kasar Afghanistan Sayyid Hamidullah Hashimi ya bayyana cewa, jamhuriyar musulunci ta Iran tan abayar da gagarumar gudunmawa ta fuskacin bunkasa ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar Afghanistan kamar yadda take taimaka mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke gudanar da harkokinsu a kasar ta hanyar gina musu cibiyoyi da masallatai da sauransu.
Kasar Iran ita ce kasa ta farko a duniya da take da gagarumin ci gaba ta fsukoki da dama daga cikin kasashen musulmi, ta yadda take taka gagarumar rawa wajen taimaka ma musulmi a duk inda suke domin su zama masu ci gaba wajen gudanar da harkokinsu an addini da kuma isar da manufofinsa ga sauran al’ummomi wadanda ba musulmi ba a duniya.
Malamin ya ce jamhuriyar musulunci ta Iran tan abayar da gagarumar gudunmawa ta fuskacin bunkasa ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar Afghanistan kamar yadda take taimaka mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke gudanar da harkokinsu a kasar ta Afghanistan.
988420
captcha