IQNA

Taron Nazari Kan Rayuwar Fatima Zahra (AS) A Kasar Iraki

9:29 - April 23, 2012
Lambar Labari: 2310407
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani dangane da rayuwar sayyida Fatima Zahra (AS) a kasar Iraki inda aka yi bayanai tare da gabatar da makaloli da aka rubuta kan rayuwarta mai albarka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar sadarwa ta Al-gadir cewa, an gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani dangane da rayuwar sayyida Fatima Zahra (AS) a kasar Iraki inda aka yi bayanai tare da gabatar da makaloli da aka rubuta kan rayuwarta mai albarka da kuma irin darussan da al'ummar musulmi za su iya dauka daga wannan rayuwa.

Da dama daga cikin masu bayanai wadanda suka hada da malaman jami'oi da kuma na cibiyoyin ilimin addini muslunci da aka fi sani da Hauza, sun gabatar da jawabansu a wannan wuri, kuma sun mayar da hnakali ne wajen hankaltar da mahalarta kan muhimmancin da ke tattare da yin koyi da abubuwan da ke cikin rayurwata, domin kuwa ita abar koyi ce ga mutane ba ki daya, ba sai mata ba kawai ko musulmi.

Gudanar da wannan zaman taro na karawa juna sani dangane da rayuwar sayyida Fatima Zahra (AS) a kasar Iraki inda aka yi bayanai tare da gabatar da makaloli da aka rubuta kan rayuwarta mai albarka, wata manuniya ce kan gagarumin sauyin da ak asamu a kasar Iraki, wanda hakan ya kasance a zamunan baya ba abu ne mai sauki ba.

991049


captcha