IQNA

Wani Dan Majalisar Dokokin Algeria Ya Keta Alfarmar Kur’ani Mai Tsarki

21:49 - April 24, 2012
Lambar Labari: 2311994
Bangaren kasa da kasa, wani dan majalisar dokokin kasar Algeria ya keta alfarmar kur’ani mai tsarki a cikin wata bababr kotu da ke birnin Aljerrs fadar mulkin kasar lamarin da ya bakanta ma daukacin al’ummar kasar inda ake yi kira da a gaggauta hukunta shi kan wannan babban laifi da ya aikata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sabr.cc cewa, wani dan majalisar dokokin kasar Algeria ya keta alfarmar kur’ani mai tsarki a cikin wata bababr kotu da ke birnin Aljerrs fadar mulkin kasar lamarin da ya bakanta ma daukacin al’ummar kasar inda ake yi kira da a gaggauta hukunta shi kan wannan babban laifi da ya aikata ba tare da wani bata lokaci ba.
Wani labarin kuma yana cewa jam’iyun adawa uku na masu kishin islama a kasar Algeria sun sanar da kafa wata babbar hadaka domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki a halin yanzu a kasar karkashin jagorancin shugaba Butaflika.
Wadannan jamiyu wadanda suka shafe tsawon lokaci suna adawa sun samu dama a wannan lokaci da ake bore a cikin wasu kasashen larabawa domin kawar da gwamnatoci ‘yan kama karya da suke yin amshin shata ga Amurka, misali daga ciki kuwa shi ne abin da ya faru akasar Masar, inda aka kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya dan koren Amurka, kuma masu kishin islama suka mamaye sha’ann mulki.
jam’iyun adawa na masu kishin islama a kasar Algeria sun dai sanar da kafa babbar hadaka ne domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki, duk kuwa da cewa masu kishin islama da suka samu mulki a Tunisia da Libya sun bayan da mummnan misali, inda suka mika kai ga turawan yamma. 991871
captcha