IQNA

Wani Bam Ya Tarwatse A Kusa Da Ofishin Jakadancin Iran A Damascus

17:51 - April 25, 2012
Lambar Labari: 2312244
Bangaren kasa da kasa, wasu 'yan ta'adda sun kai harin bam a kusa da ofishin jakandancin kasar Iran da ke birnin Damascus na kasar Syria amma hakan bai yi sanadiyar mutuwar wasu ba ko kuma jikkata.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu 'yan ta'adda sun kai harin bam a kusa da ofishin jakandancin kasar Iran da ke birnin Damascus na kasar Syria amma hakan bai yi sanadiyar mutuwar wasu ba ko kuma jikkata a wani mataki da ake bayyana shi da cewa shiryayye ne da nufin daukar fansa kan Iran.

Kasashen yammacin turai tare da aminansu Saudiyya da Qatar sun sha alwashin ci gaba da timaka ma 'yan ta'addan Syria da tarin makamai da kudade da nufin kara tashin hankali ta kasashe fararen hula, kamar yadda ake gani kullum a Syria, wanda kuma dukaknin matakan da ake kokarin dauka na sasanta bangarorin rikici na neman rushewa sakamakon abin da Saudiyya da Qatar suke yi.

Wasu 'yan ta'adda sun kai harin bam a kusa da ofishin jakandancin kasar Iran da ke birnin Damascus na kasar Syria amma hakan bai yi sanadiyar mutuwar wasu ba ko kuma jikkata, wanda hakan yazo ne a matsayin sako ga Iran da take goyon bayan samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'ummomin Syria.

993085





captcha