Bangaren kasa da kasa, ana shirin kafa wata majalisa ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kasar Masar wadda za ta taka gagarumar rawa wajen bayyana ra’yoyinsu da mahanfgarsu da kuma matsayinsu kan lamurra da dama da suka dangaci kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin kafa wata majalisa ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kasar Masar wadda za ta taka gagarumar rawa wajen bayyana ra’yoyinsu da mahanfgarsu da kuma matsayinsu kan lamurra da dama da suka dangaci kasar da siyasarta da makomarta a matsayinsu an ‘yan kasa.
Rahoton ya ce a wani bangare kuma an gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
992694