IQNA

Wasu ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Kan Cibiyar Ilimi Ta Qa’im Da Ke Birnin Karbala

21:46 - April 26, 2012
Lambar Labari: 2312641
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan ta’adda sun kaddamar da hari kan babbar cibiyar ilimi ta Qa’im da ke birnin Karbala mai alfarma da nufin firgita mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke kasar Iraki bayan da aka kasa kawar da su a siyasance a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kaddamar da hari kan babbar cibiyar ilimi ta Qa’im da ke birnin Karbala mai alfarma da nufin firgita mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke kasar Iraki bayan da aka kasa kawar da su a siyasance a kasar, wanda kuma ake zargin kasashen Saudiyya da Qatar.
A ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawan sahyuniya. 992656
captcha