Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Italia ya gana da jagororin muslmin kasar da nufin tattaunawa da su domin halin da suke ciki irin bkatun da suke da su gami da irin matsallin da suke fuskanta domin sanin hanyoyin da zai iya taimaka wa da su domin warware musu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na le tepmsdz cewa, shugaban kasar Italia ya gana da jagororin muslmin kasar da nufin tattaunawa da su domin halin da suke ciki irin bkatun da suke da su gami da irin matsallin da suke fuskanta domin sanin hanyoyin da zai iya taimaka wa da su domin warware musu ta hanyoyin da suka dace.
A wani labarin kuma jiragen yakin ruwa guda biyu mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun karasa zuwa tashan jiragen ruwa Tatus da ke kasar Syrai a yau Asabar. A yau din ne jiragen biyu suka tsallaka mashigar ruwa ta Swiz a kasar Masar suka fada cikin tekun Medeteranina, wannan dai shi ne karo na biyu a wannan shekarar wanda jiragen ruwan yaki na kasar Iran suke tsallakawa zuwa tekun Medeteranian.
Rear Admiral Habibullah Sayyari ya fadawa gidan television na PressTv wanda ke watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran cewa, manufar zuwan wadan nan jiragen ruwa shi ne bawa sojojin kasar Syria horo bisa yerjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.
Sayyari ya kara da cewa shigar Jiragen ruwan yakin kasar Iran yankin Medeterianian har'ila yau yana nuna irin karfin sojen da kasar take da shi da kuma isar da sakon zaman lafiya ga kasashen yankin.
992738