IQNA

Shugabannin Kula Da Aikin Hajji Da Likitoci Na Gudanar Da Taro A Iran

16:49 - April 29, 2012
Lambar Labari: 2314484
Bangaren kiwon lafiya: shugaban cibiyar malaman kiwon lafiya a lokutan ayyukan hajji da guraren ziyara ya bayyana cewa: shugabanni da masu kula da harkokin hajji da umara da guraren ziyara tare da likitoci masu kula da masu gudanar da ayyukan hajji da umara da ziyartar guraren ibada a karon farko na gudanar da wani taron kasa da kasa na likitoci masu kula da ayyukan hajji na kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: shugaban cibiyar malaman kiwon lafiya a lokutan ayyukan hajji da guraren ziyara ya bayyana cewa: shugabanni da masu kula da harkokin hajji da umara da guraren ziyara tare da likitoci masu kula da masu gudanar da ayyukan hajji da umara da ziyartar guraren ibada a karon farko na gudanar da wani taron kasa da kasa na likitoci masu kula da ayyukan hajji na kasashen musulmi.Said Ali Riyadi shugaban cibiyar likitocin da ayyukan hajji a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dilancin labarai na Ikna ne ya bada labarin wannan ganawa ta kasa da kasa da za a yi a tsakanin ma'aikatan kiwon lafiya na kasashen musulmi inda a lokacin wannan taro za su tattauna irin matsalolin da suke fuskanta da kuma hanyoyin da za su magance su da kuma kara kawo gyara da canjecanje a ayyukansu na kula da masu gudanar da ayyukan hajji da umara da kuma agurare na ibada da kuma yadda za kara inganta kula da masu fama da rashin lafiya daga cikinsu.
994547
captcha