IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Rufe Ofishin Jakadancin Kasar Da Ke Masar

20:08 - May 01, 2012
Lambar Labari: 2316354
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun rufe ofishin jakadancin kasar da ke birnin Alkahira na kasar Masar saboda tsananin kiyayyar da suke yi da juyin juya halin da al’ummar kasar suka yi wanda hakan ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Husni Mubarak wanda ke dasawa da gwamnatin wahabiyawan Saudiyya.
A cikin makon da ya gabata ne ministan tsaron kasar Sweeden ya mika takardar murabus dinsa bayan da ta tabbata cewa gwamnatocin Saudiyya da kuma kasarsa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa wata babbar masana’antar makamai a cikin kasar ta Saudiyya, domin yin amfani da su wajen murkushe duk wani yunkuri na neman sauyi a kasar.
A lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
995720

captcha