Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Altaghyir cewa, mahukuntan kasar Saudiya suna yin amfani da karfi da ya wuce dukaknin kaidoji da dokoki na kasa da kasa wajen murkushe fararen hula da kuma masu adawa da tsarin zalunci da danniya da kama karya na gidana sarautar kasar wadda ke dasaw ada kasashen turai da kuma yahudawan sahyuniya.
A cikin makon da ya gabata ne dangantaka tsakanin Saudiyya da Masar ta yi kamari saboda shugar shigula da kar ke a cikin harkokin Masar, wanda akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a birnin Alkahira a lokacin da wasu mutane da ake zaton magoya bayan majalisar sojin Masar ne suka akfa da makamai kan fararen hula masu adawa da mulkin soji a kasar.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga birnin Alkahira na kasar Masar ya habarta cewa, daruruwan mutane ne suke gudanar da wani zaman dirshan a gaban babban ginin ma'aikatar tsaron kasar Masar ke birnin Alkahira, inda suke kiran majalisar sojin kasar da ke mulki da ta gaggauta mika ragamar mulki ga hannun farar hula, yayin da wasu mutanen dauke da makamai suka fada musu, kuma suka kashe mutum 20 daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama.
Da dama daga cikin fitattaun 'yan siyasar kasar da suka hada da wasu daga cikin 'yan takarar neman shugabancin kasar, sun yi Allawadai da majalisar sojin kasar kan faruwar wannan lamari, yayin da wasu kungiyoyin da jam'iyyun siyasa suke yin kira da a gudanar da gagarumar zanga-zanga a ranar juma'a mai zuwa, domin yin Allah da majalisar sojin kasar.
997457