Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bilad News cewa, yan sandan gwamnatin wahabiyawan Saudiyya sun kleta alfarmar mabartar Baki’a wadda ke da kabrukan dubban sahabbai da bayin Allah wadanda suka rasu tun daga lokacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma wasu daga cikin limaman shiriya tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su da aka rufe su a wannan wuri mai daraja.
Wwasu daga cikin malaman sunna sun yi kakkausar suka kan malamin wahabiyawan Saudiyya wanda ya ci zarafin manzon Allah da addinin musulunci ta hanyar bayyana abin da ya ga dama a cikin son ransa da sunan yana bayyana matsayar addini ko kuma fatawa.
A wani labarin na daban kuma an sheda cewa kasar Siriya ta shaida cewar ba za ta janye dakarunta ba daga cikin garururwan da yan tawaye masu dauke da makamai suke, sai ta samu tabbaci daga yan bindigar a rubuce na cewar sun daina kai hare-hare, a cewar ministan harakokin wajen kasar ta Siriya a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta nuna cewa, fadar cewar kasar Siriya za ta janye daga cikin garururwan da suka mamaye kafin ranar 10 ga wannan wata ba gaskiya bane, manzon majalisar dinkin duniya da kungiyar larabawa Kofi Anan, har yanzu bai bamu tabbaci ba a rubuce na cewar sun amince da shirin na sa za su daina kai hare-haren ta'adanci daga bangaren yan adawar ba, da kuma aniyarsu ta maika makaman nasu.
Kuma Kofi Anan, bai bamu tabbaci a rubuce ba na cewar kasashe irin su Saudiya, da Turkiya, za su daina bada kudin ga kungiyoyin ta'adancin ba, wadannan kasashe sun sun taimakama yan adawar kasar ta Siriya sosai inda har kasashen irin su da saudiya ke kira a ba yan adawar makama.
A wata ganawa da shugaban kasar ta Siriya Bashar Asaad, Kofi Anan, ya shaida nauyin da aka dora masa na mutunta yancin kasar ta Siriya, kuma zai yi duk kokarin da ya dace don tsaida rikicin da ke faruwa a kasar da amsar makamai yan tawayen.
1001077