Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Romandie cewa, jam’iyyun masu kishin islama na kasar Algeria sun sanar a cikin wani bayani na hadin gwiwa da suka fitar cewa bisa ga sauraren ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar sakamakon hakan ya nuna cewa akwqai yiwuwar su samu gagarumar nasara a zabuka masu zuwa na ‘yan majalisar dokoki.
A bangare guda kuma ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan nuna tsananin kyamar da ake yi a cikin kasashen yammacin turai ga mabiya addinin musulunci tare da mayar da su saniyar ware a cikin dukaknin harkokin kasashensu saboda addininsu wanda kuma hakan ya fi tsananta ne akasashen da suke raya cewa suna kare hakkokin bil adama.
Wannan zaman taro dai zai gudana ne a birnin Arhos na kasar Danmark, kuma zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar wadanda suke da masaniya kan irin mumman tasirin da ke tatatre da nuna adawa da wani jinsi ana al’umma, kodai saboda kabilarsa ko kuma addinansa, inda za agabatar da jawabai na wayar da kai da fadakarwa.
Ko shakka babu gudanar da wannan zaman taro kan nuna tsananin kyamar da ake yi a cikin kasashen yammacin turai ga mabiya addinin musulunci tare da mayar da su saniyar ware a cikin dukaknin harkokin kasashensu saboda addininsu, yana da matukar muhimamnci musamman ga wadanda ba su da masaniya kan addinin muslunci da kuma koyarwarsa.
1003037