Bnagaren kasa da kasa, abubuwan da suke faruwa yanzu haka a cikin kasashen larabawa na bore ga azzaluman shugabanni da sarakuna hakan ya sanya da dama daga cikin mabiya addinin muslunci sun koma cikin hankalinsu tare da rungumar addininu da kuma koyarwarsa duk kuwa da cewa a da sun fara yin rauni.
Kamfann dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muslim Village cewa, masani kan harkokin siyasa da addini a kasar India Ahmad Salim ya bayya acewa abubuwan da suke faruwa yanzu haka a cikin kasashen larabawa na bore ga azzaluman shugabanni da sarakuna hakan ya sanya da dama daga cikin mabiya addinin muslunci sun koma cikin hankalinsu tare da rungumar addininu da kuma koyarwarsa duk kuwa da cewa a da sun fara yin rauni tare da daukar wasu daga cikin al'adu dab a na addininsu ba.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasa tabuka wani abin a zo a gani daga sabbin mahukuntan Libya ta fuskar kyautata rayuwar jama'ar kasar, tabbatar da tsaro da magance matsalolin tsoffin 'yan tawaye da ma dai sauran matsaloli wadanda al'ummar kasarsu ba su san su a lokacin Gaddafi ba, wannan ya tabbatar da cewa manufar kasashen turai ba ita ce kawo demokradiyya a Libya ba, musamman ma ganin cewa tun bayan kawar da Gaddafi ba su sake mayar da hankali kan halin da al'ummar kasar ke ciki ba, na kuncin rayuwa da rashin tsaro rashin shugabanci, da ma rashin sanin makomar kasarsu ta fuskoki da dama, babban abin da ya dauke ma kasashen yammacin turai hankali a Libya shi ne ayyukan da kamfanoninsu ke gudanarwa a kasar, musamman a bangaren hakar manfetur da sayar da shi, ta yadda har ta kai ga wasu daga cikin mutanen kasar sun dawo suna fifita mulkin Gaddafi a kan halin da suke ciki yanzu a kasar.
1003891