IQNA

Kungiyar Hizbullahi Ta Yi Allah Wadai da Harin Ta'addanci A Damaskos

17:11 - May 12, 2012
Lambar Labari: 2323983
Bangaren kasa da kasa: kungiyar gwagwarmaya ta musulunci a kasar Labanon hizbullahi ta fitar da wani bayani a ranar ashirin da daya ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya wanda a cikin bayanin take yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a birnin Damaskos da bamabamai day a girgiza birnin a wani mumunar manufa ta kawo cikas da yamutsi a cikin kasar ta Suriya da kuma a tsakanin al'umma.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyar gwagwarmaya ta musulunci a kasar Labanon hizbullahi ta fitar da wani bayani a ranar ashirin da daya ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya wanda a cikin bayanin take yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a birnin Damaskos da bamabamai day a girgiza birnin a wani mumunar manufa ta kawo cikas da yamutsi a cikin kasar ta Suriya da kuma a tsakanin al'umma.Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta Radion Nur a kasar Labanon day a watsa rahoton cewa: a cikin wannan sanarwa da ta fito daga kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar labanon sun yi Allah wadai da babbar murya da kuma yin tofin Allah tsine kan yadda aka kai wannan harin dabbanci da rashin tausayi a birnin Damaskos fadar mulkin kasar suriya a harin day a yi sanadiyar mutuwar fararen hula da daman gaske day a hada mata da kananan yara inda aka yi ta ganin gawarwaki da suka kaune kurmus babu kan gani da kuma abin sai tausayi da fahimtar mummunar bakar manufa ta makiya.

1004973
captcha