Bangaren kasa da kasa, an kafa wanimkwaitin bin kadun harkokin tattalin arziki bisa mahanga ta addinin muslunci a kasar Tunisia wanda zai ci gaba da gudanar da ayyukansa tare da mambobinsa wadanda masana ne kan harkokin tattalin arziki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na businessnews an kafa wanimkwaitin bin kadun harkokin tattalin arziki bisa mahanga ta addinin muslunci a kasar Tunisia wanda zai ci gaba da gudanar da ayyukansa tare da mambobinsa wadanda masana ne kan harkokin tattalin arziki daga kasar ta Tunisia.
Daga cikini muhimman abubuwan da wannan kwamiti zai mayar da hankali kansu akwai batun kafa reshen bankin muslunci a kasar, wanda yanzu haka ya fara gudanar da ayyukansu a cikin wasu kasashen ahiyar Afirka da kuma wasu kasashen musulmi da na larabawa, wanda kuma kasar Tunisia na daga cikin kasashen da ake shirin gudanar da wannan shiri na bankin muslunci.
An kafa wannan kwaiti na bin kadun harkokin tattalin arziki bisa mahanga ta addinin muslunci a kasar Tunisia da nufin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa tare da mambobinsa wadanda masana ne kan harkokin tattalin arziki na muslunci amma a zamanance.
1005038