IQNA

An Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Dalibai Na Kasashen Musulmi Da Suke Iraki

13:25 - May 14, 2012
Lambar Labari: 2325543
Bangaen kasa da kasa, daya daga cikin malaman addini kuma masani kan harkokin sadarwa ya yi kira da aka kafa wani kwamiti na dalibai masu karatun addinin muslunci da suke kasar Iraki wadanda suka fito daga kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Hojjatol Eslam Sayyid Mahdi Taqvi daya daga cikin malaman addini kuma masani kan harkokin sadarwa ya yi kira da aka kafa wani kwamiti na dalibai masu karatun addinin muslunci da suke kasar Iraki wadanda suka fito daga kasashen musulmi domin kara dankon alaka tsakaninsu, ta yadda hakan zai ba su damar yin aiki tare.
Ya ci gaba da cewa a halin yanzu dalibai daga kasashen duniya suna zuwa kasar Iraki domin yin karatu a babbar cibiyar ilimi da ke birnin Najaf mai alfarma, wanda hakan za a iya cewa ya wajabta kafa kwamiti wanda zai hada dalibai da suka fito daga kasashen musulmi, bisa la’akari da babban nauyin da ke kansu, wanda tun yanzu ne ya kamata su zama masu sanayya da juna da kuma yin aiki tare ta yadda za su amfanar da al’ummominsu a nan gaba.
Malamin wanda daya ne daga cikin malaman addini kuma masani kan harkokin sadarwa kuma shugabannin kamfanin dillancin labaran kur’ani, ya yi kira da aka kafa wannan kwamiti ne na dalibai masu karatun addinin muslunci da suke kasar Iraki wadanda suka fito daga kasashen musulmi, domin su ne malamai a lokuta masu zuwa.
1005808
captcha