Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun fito karara sun nuna cikakken goyon bayansu ga manufar masarautar Saudiyya da ke neman hade kasar ta Bahrain da Saudiyya domin murkushe yunkurin da al’ummar kasar suke domin ganin an samu sauyi ta fuskar siyasa da salon mulki a kasar wadda ta kwashe shekaru tana fama da mulkin kama karya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bisa rahotonni da ya samu daga majiyoyi masu tushe, da kuma furucin da ministan harkokin wajen Bahrain ya yi ya tabbatar da cewa mahukuntan kasar Bahrain sun fito karara sun nuna cikakken goyon bayansu ga manufar masarautar Saudiyya da ke neman hade kasar ta Bahrain da Saudiyya domin murkushe yunkurin da al’ummar kasar suke domin ganin an samu sauyi ta fuskar siyasa da salon mulki a kasar wadda ta kwashe shekaru tana fama da mulkin kama karya daga gidan sarautar Al-khalifa wadanda Amurka da Saudiyya suke mara ma baya.
A wani labarin na daban kuma daya daga cikin tsoffin 'yan kungiyar nan ta munafukai da ke fada da gwamnatin Musulunci ta Iran ta bayyana cewar kasar Saudiyya da HKI suna daga cikin masu ba wa kungiyar kudaden da take bukata wajen aiwatar da ayyukansu.
A wata tattaunawa da ta yi da shafin internet din nan na Ashraf, Maryam Sanjabi daya daga cikin 'yan kungiyar munafukan wacce ta tuba ta ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin kungiyar da gwamnatin Saudiyya, kamar yadda kuma ta ce kasar Saudiyyan ta taimaka wajen kulla alakar da ke tsakanin kungiyar da wasu jami'an kasar Jordan da nufin fadada ayyukansu na adawa da gwamnatin Musulunci ta Iran daga kasar Jordan din.
Su dai 'yan wannan kungiyar sun kafa sansaninsu ne a kasar Iraki a lokacin mulkin Saddam Husain inda daga nan ne suke kai hare-hare cikin kasar Iran da kuma tattaro wasu bayanan sirri da mika su ga makiya. A halin yanzu dai gwamnatin Irakin ta bukaci 'yan kungiyar munafukan da su bar kasar.
1007309