IQNA

Yunkurin Hade Bahrain Da Saudiyya Keta Alfarmar ‘Yancin Mutanen Kasar Ne

17:22 - May 15, 2012
Lambar Labari: 2326716
Bangaren kasa da kasa, babbar jam’iyyar adawa ta kasar Bahrain ta bayyana cewa duk wani yunkuri da mahukuntan kasar suke tare da gidan sarautar saudiyya da nufin mayar da kasar bahrain wani bangare na Saudiyya hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa da ma’yancin al’umma.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jam’iyyar Al-faq cewa, wannan babbar jam’iyyar adawa ta kasar Bahrain ta bayyana cewa duk wani yunkuri da mahukuntan kasar suke tare da gidan sarautar saudiyya da nufin mayar da kasar bahrain wani bangare na Saudiyya hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa da ma’yancin al’ummar kasar, wadda akasarinsu ba su amince da hakan ba.
Limaman masallatan juma’a a yankin gabacin kasar Saudiyya sun nuna cikakkaen goyon bayansu ga malamin da yake fuskantar barazana da mahukuntan kasar bayan da yi suka kan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar yankin katif masu neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki a kasar.
Bisa rahotonni da aka samu daga majiyoyi masu tushe, da kuma furucin da ministan harkokin wajen Bahrain ya yi ya tabbatar da cewa mahukuntan kasar Bahrain sun fito karara sun nuna cikakken goyon bayansu ga manufar masarautar Saudiyya da ke neman hade kasar ta Bahrain da Saudiyya domin murkushe yunkurin da al’ummar kasar suke domin ganin an samu sauyi ta fuskar siyasa da salon mulki a kasar wadda ta kwashe shekaru tana fama da mulkin kama karya daga gidan sarautar Al-khalifa wadanda Amurka da Saudiyya suke mara ma baya.
1007314
captcha