Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro mai taken nuna wariya da banbanci a kafofin yada labaran kasashen turai a tsakanin al’ummomi wanda zai gudana a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar, wanda wasu daga cikin sojojin sa kai na kare tsarin jamhuriyar musulunci suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
A halin yanzu akwai limaman masallatai sama da dubu takwas a fadin kasar Jmaus, kuma akasarinsu mutanen kasar Turkiya dasuke je kasar daga bangaren gwamnatin Turkiya, wadanda ba su da cikakkiyar masaniya kan harshen jamusanci. 1007870