Bangaren kasa da kasa, ma'akatr al'adu ta kasar Tunisia ta fitar da wani bayani da acikinsa ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da ayyukan dabbanci da wasu daga wahabiyawan kasar suke aiktawa na rushe muhimamn wurare masu albarka da tarihi na kasar tare da kafirta sauran musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na locote cewa, ma'akatr al'adu ta kasar Tunisia ta fitar da wani bayani da acikinsa ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da ayyukan dabbanci da wasu daga wahabiyawan kasar suke aiktawa na rushe muhimamn wurare masu albarka da tarihi na kasar tare da kafirta sauran musulmi da ba su aminta da wannan akida.
A bangare guda kuma shugaban bangaren sojin birnin Tiripoli fadar mulkin kasar Libiya Abdul-Hakim Bil-Hajj ya sanar da yin murabus daga mukaminsa domin taka rawa a fagen siyasar kasar ta Libiya, Abdul-Hakim Bil-Hajj da ya jagoranci 'yan tawayen birnin Tiripoli fadar mulkin kasar Libiya a lokacin yunkurin kifar da gwamnatin kama karya ta marigayi Mu'ammar Gaddafi ya mika takardar yin murabus daga kan mukaminsa na shugaban bangaren sojin birnin Tiripoli ga gwamnatin rikon kwaryar kasar da ma'aikatar tsaron Libiya.
Inda a ciki yake bayyana cewar ya kafa jam'iyyar siyasa domin tsayawa takara a zaben Majalisar Dokokin kasar da za a gudanar a watan Yuni mai zuwa, Abdul-Hakim Bil-Hajj shi ne tsohon shugaban Jama'atul-Islamiyya da tsohuwar gwamnatin Gaddafi ta zarga da hannu a kokarin kifar da ita da karfi, don haka tsohuwar gwamnatin kasar Birtaniya ta Tony Blair ta mika shi ga gwamnatin Gaddafi a shekara ta 2004, inda ya fuskanci dangogin azabtarwa, tare da tsare shi a gidan kurkukun Abu-Salim na tsawon shekaru 6, sannan aka sake shi a watan Maris din shekara ta 2010.
1008325