IQNA

Makircin Da Saudiyya Take Kitsawa Al'ummomin Yankin Gabas Ta Tsakiya Na Babban Hadari

21:20 - May 16, 2012
Lambar Labari: 2327699
Bangaren siyasa, makircin da gwamnatin wahabiyawan Saudiya take kitsawa al'ummomin yankin gabas ta tsakiya na tatatre da babban hadari da zai iya kaiwa ga wani rikici da ba a san karshen shi ba musamman a kasahen Syria da Bahrain.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masana da dama sun amannar cewa, makircin da gwamnatin wahabiyawan Saudiya take kitsawa al'ummomin yankin gabas ta tsakiya na tatatre da babban hadari da zai iya kaiwa ga wani rikici da ba a san karshen shi ba musamman a kasahen Syria da Bahrain inda take aikewa da 'yan tadda zuwa Syria domin kawar da shugaban kasar, yayin da take taimaka ma masarautar Bahrain domin murkushe fararen hula masu neman sauyi.
Shugaban kasar Syria Basshar Assad ya jaddada cewa: " kwararan bayanai sun tabbatar da cewa; kasashen Saudiyya da jordan suna kitsawa kasarsa makarkashiya, a yayin ganawar da ya yi da manzon m.d.d. Kofi Anan, a birnin Damascuss, shugaba Basshar Asad ya ce: "Duk wadanda su ka keta hurumin kasar Syria to za su fuskanci maida martani da ruwan makamai masu linzami, shugaban na kasar Syria ya ce: Sojojin Syira ba za su rangwantawa duk wani mai wuce gona da iri ba.

Babban makircin da gwamnatin wahabiyawan Saudiya take kitsawa al'ummomin yankin gabas ta tsakiya na tatatre da babban hadari da zai iya kaiwa ga wani rikici da ba a san karshen shi ba musamman a kasahen Syria da Bahrain wanda zai jefa yankin cikin rikici mai yawa.
1008242



captcha