IQNA

Masu Adawa A Qatar Sun Bukaci A kawo Karshen Mulkin Sarkin Kasar

18:15 - May 17, 2012
Lambar Labari: 2328048
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin iyalan gidan sarautar kasar Qatar da suke da dangantaka da sarkin kasar sun bukaci a kawo karshen mulkinsa ko ta wace hanya saboda abin da suka bayyana da cewa ya mayar da kasarsa da al’ummarta da arzikinta tamkar mallakinsa.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo naelnashra cewa, wasu daga cikin iyalan gidan sarautar kasar Qatar da suke da dangantaka da sarkin kasar sun bukaci a kawo karshen mulkinsa ko ta wace hanya saboda abin da suka bayyana da cewa ya mayar da kasarsa da al’ummarta da arzikinta tamkar mallakinsa wanda kuma acewarsu hakan dole ya kawo karshe.
An gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia tare da halartar dubban daruruwan mutane da suka gudanar da zanga-zangar goyion baya ga juyi da kuma yin Allawadai da halaratr sarkin Qatar a wurin wadannan taruka.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki Qatar a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar.
Dubban masu zanga-zanga a birnin Saqas na kasar Tunisa, sun daga kyallaye da kwallaye da aka rubuta cewa, sarki Qatar Karen farautar Amurka da yahudawa ne, saboda haka al'ummar Tunisia ba su lalae marhabin da shi a kasarsu.
1009676
captcha