Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suna taka gagarumar rawa wajen karfafa gwiwar masu akidar cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar musulmi da addinin musulunci a duniya kamar dai yadda muke gani a duniya musamman ma a cikin nahiyar turai.
an watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba duk kuwa da cewa bisa doka sai sun amince masa.
1010613