IQNA

Guguwar Canji Na Kadawa A kasar Saudiyya Domin Neman Samar Da Sauyi Na Hakika

21:04 - May 21, 2012
Lambar Labari: 2331062
Bangaren kasa da kasa, guguwar canji da ta fara kadawa akasar Saudiyya na nuni da cewa akwai gagarumin sauyi da zai faru a kasar a wasu lokuta masu nan gaba da hakan zai kawo karshen mulkin danniya da kama karya da fiir’ananci na gidan sarautar Al-saud.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na na tashar Al-alam cewa, guguwar canji da ta fara kadawa akasar Saudiyya na nuni da cewa akwai gagarumin sauyi da zai faru a kasar a wasu lokuta masu nan gaba da hakan zai kawo karshen mulkin danniya da kama karya da fiir’ananci na gidan sarautar Al-saud karnukan farautar kasashen yammacin turai da haramtacciyar kasar yahudawa.
Wasu daga cikin yahudawan sahyuniya sun fara yin kira da a saki Husni Mubarak tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a bisa zarginsa da kashe masu zanga-zangar lumana a kasar a lokacin juyin juya hali wanda ya kawo karshensa.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
1012027





captcha