Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, dan takarar kungiyar yan uwa musulmi ko kuma ikhwanul muslimin mUhammad Mirsi ne kan gaba a zaben shugaban kasa a na kasar Masar wanda kuma a ke sa ran za a je ga zagaye na biyu tsakaninsa da mai biye masa Ahmad Shafiq, wanda ya kasance tsohon pira minister a lokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak.
Jam'iyyar 'yanci da adalci ta kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Masar ta ce ta fara gudanar da tattaunawa tare da sauran bangarorin siyasa domin hada karfi da karfe a zaben da za a gudanar zagaye na biyu.
Babban sakataren jam'iyyar Isam Iryan ne ya bayyana hakan a yau a birnin Alkahira, inda ya tabbatar da cewa dan takararsu Muhammad Marsi shi ne kan gaba bisa ga abin sakamakon zaben ya yi nuni, wanda hakan zai ba shi damar karawa da mai biye masa dan takara mai zaman kansa kuma tsohon pira ministan hambararre shugaban kasar Husni Mubarak, ya ce wajibi ne su yi iyakacin kokarinsu domin kare manufar juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi.
Rahotanni sun yi nuni da cewa kasashen Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila da Saudiyya, suna ta fadi tashin ganin cewa an kayar da dan takarar kungiyar 'yan uwa musulmin, ta yadda Ahmad Shafiq babban na hannun dammar Husni Mubarak ya karbi mulkin kasar, lamarin da ya sanya wasu yin shakkun cewa akwai yiwuwar a tafka magudi a zaben zagaye na biyu ko tawace hanya, domin baiwa Ahamd Shafiq nasara. 1016008