Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na isna.net cewa za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa a Amurka wadda mabiya addinin muslunci da suke zaune a kasar za su gudanar a babban ginin cibiyar muslunci da ke birnin Washington fadar mulkin kasar ta Amurka, wadda akasarin mazauna cikinta mabiya addinin kirista ne.
adadin masallatai ya karu da kashi 74 cikin dari a kasar Amurka kamar dai yadda wani rahoto ya nuna wanda kungiyar jama’at Iman ta watsa a yau da ke cewa wannan adadi ya karu ne a cikin shekaru goma da suka gabata har zuwa karshen shekara ta 2011.
A cikin shekara ta 2000 masallatan da suke fadin kasar amurka a cikin dukkanin jahohi hamsin na kasar adadin bai wuce 1209 ba, amma ya zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya adadin ya karu kashi saba’in da hudu idan aka kwatanta da wancan adadin, in da ya kai masallatai 2106 a cikin jahohi hamsin na kasar.
Wani bangare na wannan rahoto an yi ishara da cewa, mafi yawan matasa mabiya addinin muslunci mazauna kasar Amurka, sun yi amannar cewa manyan jami’an gwamnatin kasar suna tsananin gaba da addinin muslunci da koyarwarsa, amma hakan ba zai hana su ci gaba da gudanar da harkokinsu na muslunci ba.
A irin wannan yanayi day adaga cikin majalisar shura ta musulmin Amurka ya ce duk da matsin lamabar baya-bayan nan, an karbi mabiya addinin muslunci a cikin al’ummar Amurka duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye.
1016705