IQNA

Taron Tunawa Da Marigayi Imam Khomeni (QS) A Birnin Pretown

21:37 - June 02, 2012
Lambar Labari: 2339521
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Pretown na kasar saliyo da nufin tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin gwagwarmaya da makiya muslunci da all’ummar musulmi na duniya baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa an gudanar da wani zaman taro a birnin Pretown na kasar saliyo da nufin tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin gwagwarmaya da makiya muslunci da all’ummar musulmi, kama daga sarki Shah har zuwa babban shaidan da kuma haramtacciyar kasar yahudawa.
Bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni da muke cikinsa.
A yayin wannan taro za a gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana gami da malaman jami’oi da maruta za su gabatar, inda za a yi bayani kan matsayinsa na ilimi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, wadanda suke danne sauran al’ummomin duniya tare da dora manufofin siyasarsu kan duniya bisa zalunci.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni na dubu biyu da muke ciki. 1021123
captcha