IQNA

Wani Bam Ya Tarwatse A Kusa Da Gidan Sayyid Muktada Sadr A Najaf

17:37 - June 04, 2012
Lambar Labari: 2339907
Bangaren kasa da kasa, wani bam da aka dana a kusa da gidan sayyid Muktada Sadr da ke cikin Najaf Ashraf ya tarwatse bayan da aka tayar da shi daga nesa lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutanen da suke kusa da wurin a lokacin da abin ya faru.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na radiosawa cewa, wani bam da aka dana a kusa da gidan sayyid Muktada Sadr da ke cikin Najaf Ashraf ya tarwatse bayan da aka tayar da shi daga nesa lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutanen da suke kusa da wurin a lokacin da abin ya faru kamar dai yadda rahotanni da kuma shaidun gani da ido suka tabbatar.
miliyoyin mutane sun gudanar da zanga-zanga adukkanin biranan jamhuriyar muslunci ta Iran da suka hada da birnin Tehran fadar mulkin domin nuna rashin amincewa da makircin Amurka na hada kasar Bahrain da kuma kasar saudiyya bayan da suka kasa murkushe yunkurin neman sauyi da al’ummar kasar ke yi ta hanyar lumana sama da shekara guda.
Masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana a fadin kasar ta Bahrain.
Gungun 14 ga watan Fabrairu da ke jagorantar boren neman sauyi a Bahrain, wanda dukkanin bangarori na kasa da kasa suka tabbatar da cewa sama da kashi tamanin cikin dari ne suke gudanar da wannan bore, gungun ya fitar da wani bayani da ya yi kakakusar suka a cikinsa, dangane da yadda wadannan kasashen suke nuna banbanci tsakanin al’ummomin larabawa.
1022112


captcha