Kmafanin dillancin labaran iqna ya zanta da wani daya daga cikin masana a birnin London na kasar Birtaniya Talib Awwad wanda ya bayyan acewa, jagoran juyin juyta halin muslunci kuma mu’assin jamhuriyar muslunci ta Iran marigayi Imam Khomeni (RA) ya samu asalin tunaninsa ne dag amakarantar Imam Hussain (AS) inda ya koyi rashin mika kai ga zalunci da danniya ta makiya muslunci tare da yin kira zuwa ga tabbatar da adalci karkashin shari’ar Allah madaukakin sarki.
A bangare guda kuma an bayyana cewa masana da manazarta za su gudanar da wani taron da aka yi wa take da ranar Ali (AS) a birnin Lkhu na kasar India wanda zai daidai da ranar da ake gudanar da bukukuwa na haihuwar Imam Amirul muminin (AS) a dukkanin kasashen duniya domin raya wannan rana mai albarka.
Malaman addinin muslunci a kasar Iraki sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan miliyoyin mutanen da suka gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a yankunan kasar Iraki domin kawo cikas ga wadannan taruka.
Miliyoyin mutane ne su ke ci gaba da juyayin zagayowar kwanaki 40 na ashura a birnin Karbala na kasar Iraki, rahotannin da su ke fitowa daga Karbala sun ce ana hasashen cewa mutanen da su ka cika birnin sun haura miliyan 10, da su ka hada mutanen kasar da kuma bakin da su ka zo daga kasashen makwabta.
Miliyoyin Irakawa ne dai su ka ti tattaki da kafafunsu daga garuruwa masu nisa domin zuwa karbala.
A gefe daya 'yan ta'adda sun rika kai hare-gare ga masu tafiyar zuwa karbala sai dai hakan bai hana mutane ci gaba da azamar isa hurumin imam Hussain (a.s.) ba, a yau ma mutane 20 ne su ka yi shahada saboda harin da wani dan kunar bakin wake ya kai musu a garin Basra.
1022258