IQNA

Karatun Kur’ani Na Da Gagarumin Tasiri Wajen Ciratar Da Ma’anarsa

23:22 - June 05, 2012
Lambar Labari: 2340700
Bangaren kasa da kasa, karatun kur’ani mai tsarki da kyautata shi yadda ya kamata tare da kiyaye dokoki da ka’idojinsa yana bababn tasiri wajen ciratar da ma’ana zuwa ga mai saurare ta yadda zaiu fahimci ma’ana cikin sauki yana mai tasirantuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wata zantawa da ta hada shi da wani makarancin kur’ani Dr. Ammar Mu’allim ya bayyana cewa karatun kur’ani mai tsarki da kyautata shi yadda ya kamata tare da kiyaye dokoki da ka’idojinsa yana bababn tasiri wajen ciratar da ma’ana zuwa ga mai saurare ta yadda zaiu fahimci ma’ana cikin sauki yana mai tasirantuwa da shi ta hanayar jin kira’a.
Ana shirin fara gasar kur’ani a mataki na karshe na jami’ar Mostafa (SAW) tare da halartar wakilin jagoran juyin juya halin muslunci bababr cibiyar kula da harkokin wadanda suka shada da sadaukantarwa a lokacin da kasar ta yi fama da yaki wanda ak akallafa mata tsawon shekaru takwas.
A bangare guda kuma fitaccen malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu da kuma muggan sarakuna da suke mulkar al’umma bisa tsari na zalunci da danniya.
Malamin ya bayyana hakan a wagaban wani babban taro da aka kira na tunawa da ranar shahadar Imam bakir Sadr a birnin Najaf mai alfarma, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniyar musulmi da ma kasashen Asia da dama, gami da manyan malaman addini da na jami’oi na kasar Iraki, inda ya bayyana siffofinsa da cewa mutum ne da ya sadaukantar da ransa saboda Allah da kuma daukakar addinin Allah.

1015050



captcha