IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Rayuwar Marigayi Imam Khomeini (RA)

13:53 - June 06, 2012
Lambar Labari: 2341169
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro na kasa da kasa kan rayuwar marigayi Imam Khomeni (RA) a birnin Tehran tare da halartar manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini gami da masana da suka zo daga kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, a jiya an gudanar da zaman taro na kasa da kasa kan rayuwar marigayi Imam Khomeni (RA) a birnin Tehran tare da halartar manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini gami da masana da suka zo daga kasashen ketare da suka gabatar da jawabai da kuma makaloli kan hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Aya. Sayyeed Alyul Khaminaee ya bayyana yunkurin da mutane a kasashen Larabawa daban daban suke yi tabbatar da "yencin kasashensu da kuma adalci a kasashensu, suna yin hakan ne karkashin inuwar addinin Musulunci, Jagoran ya bayyana haka ne a yau lahadi, a jawabin da ya yi wa dimbin mutanen da suke juyayin wafatin Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a hubbarensa da ke kusa da Makabartan Beheshti Zahra da ke kudancin birnin Tehran.
Aya. Khaminaee ya kara da cewa, da yardar Allah yunkurin musulmin wadannan kasashe zai kai ga nasara, kuma kasashen yankin gabas ta tsakiya musamman na kasar Iran suna da kekkyawar makoma nan gaba, daga karshe jagoran ya yi kira ga wadannan kasashe su kaucewa fadace fadacen kabilanci da bangaranci ko kuma na addini, wadanda sukan kawo cikas a nasarorin da suke samu kan azzaluman shuwagabanninsu.
1023401

captcha