Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai an kafa wata jam’iyyar siyasa ta muslunci a kasar Libya karkashin jagirancin Bilhaj tsohon shugaban majalisar soji ta birnin Tripoli wanda ya kasance kan gaba wajen yakar tsohuwar gwamnatin Gaddafi har zuwa kawo karshenta a cikin watan Agustan da ya gabata.
Wani labarin kuma Mansur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi kamar yadda ake gani a duk inda suka wata kungiya ko cibiya, a cikin kasashen musulmi da ma kasashen da ba na musulmi ba.
Ya ci gaba da cewa dle ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin takawa ‘yan salafiyya burki kan ayyukansu na wuce gona da iri, tare da kara fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaurace ma su neman fitina acikin al’ummar musulmi, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai kawo zaman lafiya a cikin al’umma.
Masur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi, domin kawai su cimma manufofinsu, ko kuma zatra da manufofin wasu bisa sani ko bisa jahilci.
1023264