Bangaren siyasa da zamantakewa, tsoron Allah madaukakin sarki da daukar rayuwa mai sauki su ne babban sirrin nasarar da Imam Khomeini (RA) ya samu a cikin dukkanin lamurransa na rayuwa da kuma kaiwa ga kafa jamhuriyar muslunci wadda ta zama irinta ta farko a duniyar da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio cewa, Muhammad Hussain Abidini yana cewa tsoron Allah madaukakin sarki da daukar rayuwa mai sauki su ne babban sirrin nasarar da Imam Khomeini (RA) ya samu a cikin dukkanin lamurransa na rayuwa da kuma kaiwa ga kafa jamhuriyar muslunci wadda ta zama irinta ta farko a duniyar da muke ciki a wannan karni.
Wannan sakamako ne bayan gudanar da taruka kan cika shekaru ashirin da uku da rasuwarsa, inda aka gudanar irin wadannan taruka a kasashen duniya daban-daban kuma aka gabatar da laccoci da gabatar da makaloli wanda malamai da masana suka rubuta kan rayuwarsa da dukaknin bangarorinta, inda akasarinsu suka hadu a kan muhimman abubuwan da rayuwarsa ta shahara da su.
Mahangar mafi yawan mutane ta zo daya dangane da marigayi Imam Khomeini (RA) kan lamurra da dama da hakan ya hada matakan rayuwearsa na neman ilimi da gwagwarmayarsa da azzaluman duniya da kuma tasirin hakan wanda ya kawo gagarumin canji a duniya, musamman ma bayan samun nasarar juyin juya halin da ya jagoranta.
1025077