IQNA

An Yi Allawadai Da Shigar Shugular da Saudiyya Ke Yi Cikin Harkokin Iraki

20:33 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344585
Bangaren kasa da kasa, an yi Allawadai da shigar shugular da kasar Saudiyya ke yi cikin harkokin kasar Iraki da nufin tarwatsa kasar a siyance da kuma neman haddasa rikicin da zai kai ga komawar kasar ga yakin basasa ko na mazhaba a nan gaba duk da cewa masana suna ganin cewa Saudiyya ba za ta yi nasara kan hakan ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na radiyon Iraki cewa, a sassa na kasar Iraki dubban mutane sun yi zanga-zangar yin Allawadai da shigar shugular da kasar Saudiyya ke yi cikin harkokin kasar Iraki da nufin tarwatsa kasar a siyance da kuma neman haddasa rikicin da zai kai ga komawar kasar ga yakin basasa ko na mazhaba a nan gaba duk da cewa masana suna ganin cewa Saudiyya ba za ta yi nasara kan hakan ba, bisa la’akari da matsayar da ‘yan siyasa da dama suka dauka na kin maincewa da wannan makirci.
A Masar kuwa an gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
1026527


captcha