Kamfanin dillancin labaran iqna y habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo ncewa, day daga cikin malaman addini Hussain Sabiri ya bayayana cewa mutane a wannan zamani na da matukar bukatuwa zuwa ga tsari na addini irin wanda marigayi Imam khomeini (RA)) ya kafa a kasar Iran tare da taimakon Allah madaukakin sarki da kuma goyon bayan mutane, wanda hakan ya zama tsari abin koyi ga kasashe da dama.
Imam Khomeini (RA) ya kasance mutum na farko a cikin wannan karni da ya kafa kasa mai tsari irin na muslunci kuma ya yi daidai da yadda duniya take tafiya,duk kuwa da matsin lamba da makirci da ake shirya ma wannan kasa, amma ta ci gaba da kasancewa kan tafarkin da ya kafa ta addini da kuma tsarin siyasa madaidaici.

A bangare guda kuma ya ce gwamnatin wahabiyawan Saudiyya ta kirayi wani zaman taro na mabiya addnai da al’au na kasashen duniya da sunan yunkurin samar da fahimtar juna tsaknain dukkanin al’ummomi wanda ake ganin cewa hakan ya yi hannun riga baki daya da abin da gwamnatin kasar take aikatawa kan marassa rinjaye a kasar, wanda kuma yin adalci da daidaito tsakanin mutane zai kawo fahimtar juna akasar.
limaman masallatan juma’a a yankin gabacin kasar Saudiyya sun nuna cikakkaen goyon bayansu ga malamin da yake fuskantar barazana da mahukuntan kasar bayan da yi suka kan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar yankin katif masu neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki a kasar.
1026070