Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, al’ummar kasar Iran sun taka gagarumar ta fuskar fadakar jama’a a yankin gabas ta tsakiya musamman ma kasantuwar yunkurin da mutane suke yana da danganta da akidar musulunci da kuma kiyayya da zalunci da haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya da ke danne tare da zaluntar al’ummomin yankin.
Ali Asgar Sultaniyye ya ce aikin hukumar IAEA shi ne bincike da kuma sanya ido akan ayyukan makamacin Nuclear a kasashen duniya, ammam a halin yanzu ta zama kafa ta musamman na liken asiriwa ga wasu kasashen yamma, inda take bawa wadannan kasashen rahotannin da suka shafi kasar Iran, wadanda kuma basa da dangantaka da ayyukanta. A wani lokacin hukumar takan amince ta kuma yada rahotanni dangane da shirin makamanin nuclear kasar Iran wanda babu tabbaci a kan ingancin su.
Sa'eed Jalili shugaban majalisar koli ta tsaron kasa a nan iran, a wata wasikar da ya rubutawa Katrina Ashton wakiliyar kungiyar tarayyar turai na harkokin waje, ya bayyana mata cewa halayen da wasu kasashen yamma suke nunawa kan kasar Iran, suna barazana ga samun nasarar tattaunawan kasar Iran su a birnin Mosco.
Jalili ya kara da cewa, daga cikin wadannan halaye akwai kokarin dorawa kasar Iran sabbin takunkumin tattalin arziki daga bangaren su wadannan kasashe su kadai, kashe masanen ilmin fasahar nuclea na kasar Iran da kuma kokarin maida batun shirin nuclear kasar Iran ga komitin tsaro na MDD.
Daga karshe dai masana da dama suna ganin idan yadda shugaban hukumar ta IAEA a halin yanzu Yokiya Amano yake tafiyar da ayyukan hukumar ya ci gaba, to kuwa wannan zai shafi mutuncinta, ya kuma rage darajarta a idanun kasashen duniya da dama. Har'ila yau hakan zai bayyana raunin da hukumar take da shi a ayyukan da yakamata ta aikata, kuma abin kunya ne a gareta.
1027248