Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, makomar siyasa a kasar Libya na cikin wani yanayi na rashin tabbas domin kuwa abubuwan da suke faruwa yanzu a kasar wata babbar manuniya ce kan haka kasantuwar mutanen da suke rike da lamurran kasar masu biyayya ne ga manufofin turawa kuma ashirye suke su kare wadannan manufofi sabanin abin da mutanen kasar suke tsammani ta yadda har wasunsu suka mara musu baya domin kawar da Gaddafi.
Hukumar zaben kasar Libya ta bakin shugabanta Nouri Al-Abbar, ta bayyana cewa sai a ranar 7 ga watan Yuli mai zuwa ne idan Allah ya kai mu za a gudanar da zaben Majalisar da za ta rubuta wa kasar sabon kundin tsarin mulki, kuma dage zaben ya samo asali ne daga wasu matsaloli masu nasaba da rashin kammala ayyukan tantance sunayen mutanen da suka cancanci jefa kuri'a a wannan zabe wanda shi ne na farko da za a gudanar a kasar da ke kokarin dora kanta a kan turbar dimokuradiyya bayan kawar da Kanar Mu'ammar Kaddafi daga karagar mulki.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake dage ranar gudanar da wannan zabe a kasar ta Libya ba, wanda kuma gudanar da shi zai iya kansacewa wani ma'auni da zai fayyace matsayin gwamnatin rikon kwaryar kasar wadda kasashen Turai da Amurka da kuma wasu kasashen Larabawa suka yi ruwa da tsaki wajen ganin cewa an kafa ta a daidai lokacin da tsohon shugaban kasar Kanar Kaddafi yake zaune daram a cikin fadarsa ta Babal Azaziyya da ke birnin Tripoli.
Duk da cewa a wannan karo Nouri Al-Abbar ya ce an dage gudanar da zaben ne sakamakon rashin kammala aikin tantance masu jefa kuri'a, to amma a cikin kwanakin da suka gabata ya taba cewa tuni hukumarsa ta yi wa mutanen kasar milyan 2 da dubu 700 wannan rejista, wato fiye da 80% na wadanda ya kamata a yi wa rejistar, inda kuma ya ce ba makawa za a gudanar da zaben kafin ranar 19 ga wannan wata na yuni.
Karkashin dokokin sabuwar kasar ta Libya dai, wannan sabuwar Majalisa da za a zaba tana da wakilai 200 ne da za su fito daga bangarori daban daban na kasar, sannan kuma babban aikin Majalisar shi ne rubuta wa Libya sabon kudin tsarin mulki wanda zai fayyace karfin ikon sabon shugaban kasa da kuma sabuwar Majalisar dokokin da za a zaba a nan gaba da kuma karfin ikon kowanne daga cikinsu.
Daga cikin wakilai 200 da za su gudanar da wannan gagarumin aiki, kujeru 120 an ware su ne ga 'yan takara masu zaman kansu, yayin da sauran kujeru 80 aka ware wa sabbin jam'iyyun siyasar kasar domin yin takara a kai. A cewar hukumar zaben ta Libya, mutane fiye da dubu 4 ne suka gabatar mata da takardunsu na takarar wadannan mukamai.
T o sai dai a karkashin dokar zabe ta kasar da shugaban gwamnatin rikon kwarya Mustafa Abduljalil ya sanya wa hannu a cikin watan Janairun da ya gabata, duk wanda ya taba rike wani mukamin gwamnati a lokacin mulkin Kaddafi, ko wanda ya riki wani mukami a kwamitin juyin juya hali tun daga matakin uguwa har zuwa mataki na kasa a lokacin mulkin na kanar Kaddafi, to irin wadannan mutane an haramta masu tsayawa takara a wannan zabe da kuma sauran zabuka da za su biyo baya.
1027601