IQNA

Farfaganda Kan Iran Na Da Babbar Tazara Da Abin Da Shi Ne Gaskiyar Lamari

20:29 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346736
Bangaren siyasa da zamnatakewa, wani malamin jami’ar birnin Manilla na kasar Philipines ya bayyana cewa ana yayata karya da farfangada dangane da jamhuriyar musulunci ta Iran a duniya musamman a kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai da ‘yan korensu amma kuma hakikanin lamarin bah aka ba ne.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yada labaransa na bangaren nahiyar Asia cewa, Bai Badou wani malamin jami’ar birnin Manilla na kasar Philipines ya bayyana cewa ana yayata karya da farfangada dangane da jamhuriyar musulunci ta Iran a duniya musamman a kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai da ‘yan korensu amma kuma hakikanin lamarin ba haka ba ne idan da mutane za su kasar su hakinain gaskiya.
A wani labarin kuma Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da cewa ta samu nasarar kama wasu daga cikin mutanen da suke da hannu cikin kisan gillan da ake yi wa masanan nukiliyan kasar cikin 'yan shekarun nan.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na Iran ya bayyana cewar, a cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirrin ta fitar a yau din nan alhamis, ta bayyana cewar: Jami'an tsaron ma'aikatar sun sami nasarar kama wasu daga cikin mutanen da suke da hannu wajen kisan gillan da aka yi wa Mustafa Ahmadi Roshan daya daga cikin masanan nukiliyan kasar Iran da aka kashe a watannin baya.
Sanarwar ta bayyana cewar: Jami'an tsaron sun sami nasarar kame wadanann mutane ne bayan bayanan sirrin da suka samu kansu sannan kuma tuni ana ci gaba da gudanar da bincike kansu. Kamar yadda kuma ma'aikatar da sanar da cewa ba za ta taba yin kasa a gwuiwa ba wajen kamo da kuma hukumta dukkanin wadanda suke da hannu cikin kashe masanan Iran.
A ranar 11 ga watan Fabrairun wannan shekarar ta 2012 ne wasu 'yan ta'adda da suke da alaka da HKI suka kashe shahid Mustafa Ahmadi Roshan, daya daga cikin masanan nukiliyan kasar Iran a kokarin da suke yi na dakatar da shirin da kuma irin nasarorin da Iran take samu a wannan bangaren.
1029478
captcha