IQNA

Bom Ya Tashi A Kan hanyar Masu Ziyarar Musa Kazim (AS) A Bagdad

20:28 - June 14, 2012
Lambar Labari: 2346738
Bangaren kasa da kasa, wani bam da ‘yan ta’adda suka dana a kan hanyar masulmi masu ziyarar Imam Musa Kazim (AS) jikan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbabata a gare shi lamarin da ya yi sanadiyar shahadar wasu da kuma jikkatar wasu daga cikin wadanda ke wurin.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalato dag shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al’alam cewa, a jiya wani bam da ‘yan ta’adda suka dana a kan hanyar masulmi masu ziyarar Imam Musa Kazim (AS) jikan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbabata a gare shi lamarin da ya yi sanadiyar shahadar wasu da kuma jikkatar wasu daga cikin wadanda ke wurin domin haddasa rikici a kasar na banbancin mazhaba.
Hare haren ta'addanci da aka kai a sassa daban daban na kasar Iraki sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 60 tare da jikkatan wasu fiye da dari na daban a yau laraba, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta bayyana cewa: Hare haren ta'addanci ta hanyar tada motoci biyu da aka makare da bama bamai a garin Hilla sun lashe rayukan mutane akalla 22 tare da jikkata wasu da dama, har ila yau tarwatsewar wasu motoci hudu da aka cika da bama bamai tare da kai hari ta hanyar harbi sun lashe rayukan mutane akalla 18 tare da raunata wasu masu yawa a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki.

kuma an kai hare haren ne kan tawagar mutanen da suke kan hanyarsu ta ziyartar wajaje masu tsarki, Haka nan an kai hari ta hanyar tarwatsa motoci biyu a garin Balad da suka yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla 4, kamar yadda hare haren suka jikkata wasu da dama.

1029373


captcha