Kmafanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, birnin Daka na kasar Bangaladash ne birnin al’adun muslunci na shekara ta 2012 wanda kuma zai dauki nauyin bakuncin taron da za a guanar na sanar da wannan matsayi da zai samu halartar wakilai daga kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen mulmi na duniya baki daya.
A wani rahoton kuma a yau yahudawan sahyuniya sun rufe kofar shiga masallacin Qods domin hana palastinawa yin sallah a cikinsa hakan ya zo ne a wani mataki da mambobin jamiyar likud ta masu tsatsauran ra’ayi daga cikinsu ta dauka domin tsokanar musulmi mazaunan birnin, da sauran musulmi masu sauran lamiri a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
1029090