IQNA

Samar Da Fahimtar Juna Da Haduwar Kamla Guda Ita ce Manufar Hizbullah

18:38 - June 15, 2012
Lambar Labari: 2347111
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar manufar kungiyar ita ce samar da hadin kai da fahimtar juna tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba domin kaiwa ga manufa guda ta samun tabbatar da tsaro a kasar Lebanon baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar da ke watsa shirinsa kan tauraron dan adam daga birnin Beirut na kasar Lebanon cewa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmayar hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa babbar manufar kungiyar ita ce samar da hadin kai da fahimtar juna tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba domin kaiwa ga manufa guda ta samun tabbatar da tsaro a kasar Lebanon baki daya, tare da fahimtar bababn hadarin da ke fuskantar dukkanin al’ummar musulmi da na larabawa.
Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanan Sayyid Hassan nasrullah ya jadadda goyon bayansa ga jagoran juyin juya halin muslunci da kuma shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran kan gagarumar gudunmawar da suke bayarwa adukaknin bangarori na ci gaba n al’ummar musulmi.
Kasar Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran. Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar. Ayatullah Ali Khamenei, ya kara da cewa, Wasu bangarori sun yi ta kokarin nuna cewa kasar Iraki, ba ta da wani matsayi a cikin kasashen larabawa, amma bayan taron kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudana a Bagdada, kasar Iraki, a yanzu na kan gaba a cikin wannan kungiyar, kuma praministan kasar ke jagorantar ta.
1028974




captcha