IQNA

Gidan sarautar Saudiyya Ne Ke Goyon Bayan Tsoffin Jami’an Gwamnatin Mubarak

15:48 - June 17, 2012
Lambar Labari: 2348796
Bangaren kasa da kasa, ofisoshin jakadancin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin Alkahira na kasar Masar ne suke goyon bayan dan takarar neman shugabancin kasar Masar Ahmad Shafiq kuma tsohon pira ministan kasar karkashin gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa, ofisoshin jakadancin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin Alkahira na kasar Masar ne suke goyon bayan dan takarar neman shugabancin kasar Masar Ahmad Shafiq kuma tsohon pira ministan kasar karkashin gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar wanda aka kawar da gwamnatinsa ta hanaya juyin juya hali.
ana shirin gudanar da zaben shugfaban kasar Masar zagaye na biyu tsakanin ‘yantakara biyu na kungiyar Ikhwanul muslimin da kuma Muhammad marsi da kuma mai zaman kansa kuma tsohon pira minista alokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak Ahmad Shafiq wadanda dukakninsu suka samu kuri’u fiye da na sauran a zagayen farko.
Masu zabe sun fito a rana ta biyu don zaben shugaban kasa a kasar Masar a yau Alhamis. Duk da cewa wasu suna ganin fitowar masu zaben shugaban kasa a jiya laraba bai kai na zaben yan majalisar dokokin kasar ba. Amma duk da haka fitowar tana da yawa har sai da wasu suka kasa kada kuri'arsu a jiya don yawan masu zabe, don haka ne suka fito a yau don kada kuri'arsu.
Babu wanin tashin hankali da ya faru a zaben a jiya dai, inda banda duwatsu da takalma da aka jefa kan dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon Priminister a lokacin Mubarak wato Ahmad Shafiq, a lokacin da ya je rumfan zabe don kada kuri'arsa.
Kungiyar Ikhwanul muslimin dai ta bada sanarwan cewa dan takararta Muhammad Mursi, shi ne a gaba, hakama masu goyon bayan Amru Musa sun bayyan cewa dan takarar ikhwanul muslimin ne a gaba sannan dan takaransu Amru Musa yana biye da shi. 1030973
captcha