Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masana da dama sun imanin cewa duk da cewa sa’ad Hariri da Samir ja’aja sun kaurace ma zaman tattaunawa na kasa da shugaban kasar Lebanon ya kira afadarsa da ke birnin Beirut fadar mulkin kasar amma halartar wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar kasar da suke da ra’ayi iri da suka goyi bayan gwagwarmaya hakan ya tabbatar da nazasara ga wannan gwagwarmaya ta mutanen kasar karkashin jagorancin kungiyar Hizbullah.
An kafa wani kwamiti na bincike kan harkokin palastinawa ‘yan gudun hijira wanda zai gudanar da zamansa a birnin Alkahira na kasar Masar a cikin wannan mako a babban ginin kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ke cikin birnin.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
Kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa irin su Saudiyya da sauransu.
1029490