Kamfanin Dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, zaman taro na karawa juna sani kan watan ramadan mai alfarma da kumamuhimman ayyukan da ake yi a cikinsa a Sen denis na kasar Faransa wanda a ka saba gabatarwava kowace shekara kafin shigar watan ramadan mai alfarma da aka saba gudanarwa domin kara fadakar da musulmin kasar.
Gungun lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin fararen hula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wakilai daga kasashen Iran, Yeman, Saudiyya, Lebanon, Morocco, Tunisia, Turkiya, Aljeria, Libya, Oman da kuma Qatar, wadanda dukakninsu mambobi ne akungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, wadda ta take wakiltar musulmi a taruka na kasa da kasa.
Kungiyar lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin mutane, duk kuwa d cewa ra’ayoyi kan boren larabawa sun sha banban.
1031784