Bangaren kasa da kasa, kimanin mutane 32 aka tabbatar da sun yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai kan masu ziyarar Imam Musa Kazim (AS) a birnin Bagadaza tare da jikkatar wasu masu tarin yawa a kokarin da wahabiyawa suke yi na ganin sun hana duk wani aikin ibada da suke ganin ya yi hannun riga da fahimtar su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa kimanin mutane 32 aka tabbatar da sun yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai kan masu ziyarar Imam Musa Kazim (AS) a birnin Bagadaza tare da jikkatar wasu masu tarin yawa a kokarin da wahabiyawa suke yi na ganin sun hana duk wani aikin ibada da suke ganin ya yi hannun riga da fahimtar su ta kafirta sauran musulmi.
Sabuwar dokar da aka kafa a kasar Saudiyya dangane da wajabta ma mutane dakatar dukkanin ayyukansu a lokacin salla a kasar Saudiyya hakan ya jawo rikici a tsakanin mutanen kasar da kuma mahukunta, sakamakon matakan da gungun mutanen da ake kira masu hani daga mummna da umurni da kyakkayawa suke aikatawa da sunan suka kare addini tare da izini daga masarautar wahbaiyawan kasar.
A lokacin da malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
1031697