IQNA

Musulmin Amurka Sun Nuna Rashin Gamsuwarsu Da Takura Musu Da Ake Yi

21:10 - June 19, 2012
Lambar Labari: 2350122
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke dauka a kansu ta hanyar takura musu da tura musu masu aikin leken asiri wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na ‘yan kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Onislam cewa mabiya addinin muslunci a kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke dauka a kansu ta hanyar takura musu da tura musu masu aikin leken asiri wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na ‘yan kasa amma su musulmi ana mu’amala da su kamar ba ‘yan kasa ba.
a wani bayani da ya gabatar a gidan talabijin din kasar Faransa a zantawar da ta hada shi da gidan talabijin shugaban kasar Nikola Sarkozy ya bayyana cewa ba su lalae marhabin da Yusuf Qardawi bisa zarginsa da tunzura mutane wajen aikata ayyukan ta’addanci da kuma tsatsauran ra’yi, wanda a cewarsa Faransa ba ta amince da hakan ba.
Shugaban kasar ta Faransa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wata zantawa tare da sarkin kasar Qatar wanda daya ne daga cikin amintattu ga kasar Faransa, kuma shi ne wanda ya ajiye Qardawi a kasar bayan mahukuntan Masar sun kore shi sakamakon matakan da yake dauka na tunzura mutane zuwa tsatsauran ra’ayi, wanda kuma hakan ya kawo rashin jituwa tsakanin Qatar da Masar.
A cikin ‘yan lokutan nan dai Qardawi ya fitar da fatwoyi na kafirta mutane da suka hada da fatawarsa kan Husni Mubarak a lokacin da mutane suna bore a kasar Masar, haka nan kuma ya kafirta Gaddafi da kuma shugaban kasar.
1030957

captcha